yan sanda

‘Yan Sanda Sun Hallaka ‘Yan Fashi Uku A Anambra

Rahotanni daga jihar Anambra sun tabbatar da cewa jami’an tsaron ‘yan sandan Nijeriya sun hallaka ‘yan fashi da makami uku a ranar Alhamis bayan musayar wuta da aka yi tsakanin jami’an ‘yan sandan da wadanda ake zargin cewa ‘yan fashi da makamin ne a Federal Housing Estate Fegge, dake Onitsha.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitarwa da manema labarai a garin Awka.

Mohammed, ya ce wadanda aka kashe din duka maza ne, sai dai har yanzu ba a gano wani bayani dangane da su ba. Sai dai ya ce sun yi nasarar cafke mutum biyu suma da ake zarginsu da fashi da makamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *