A halin da ake ciki yanzu haka, mawallafin Jaridar nan ta Sahara Reporters kuma dan rajin kare hakkin Bil’adama wato Omoyele Sowore na chan asibiti yana karɓar magani bayan da yan sanda suka fesa mishi barkonon tsohuwa a yau Litinin.
Ɗaya daga Lauyoyin Sowore mai suna Inibehe Effiong ita ta sanar da haka, inda ta ce wata jami’ar yar sanda ce ta fesa masa barkonon tsohuwar yayin da yake jagorantar wata zanga-zanga a dandalin Unity Fountain dake birnin tarayya Abuja.
Ko da yake majiyoyi da dama sun bayyana cewa ɗaya daga kwanson hayaki mai sa hawayen ne ya zarce ya samu Sowore,, to amma Effiong ta bayyana cewa kai tsaye da aniya aka harba, lamarin da ya kai ga ya jikkata shi.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano cewa Kwamishinan yan sandar birnin tarayya Abuja da kan shi ya kasance wurin zanga-zangar tare da sulke don kare kai daga hare-haren masu zanga-zangar.