Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kama wani mutum mai suna Vincent Sampson Enuneku da ke bayyana kansa a matsayin mataimakin Sufeton ‘yan sanda wajen aikata munanan ayyuka a jihar., kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Odiko Macdon ya fitar kuma wakilin Majiyar jaridar Dimokuradiyya a Uyo ya samu a ranar Talata, ta ce wanda ake zargin dan shekara 43 daga karamar hukumar Ndokwa ta jihar Delta, ya yi kaurin suna wajen gabatar da shaidar karya na aikin dan sanda, a wuraren bincike yayin da kuma ya ke jigilar tabar wi-wi da sauran abubuwan da aka haramta a cikin jihar.
Sanarwar ta kara da cewa wanda ake zargin yana amfani da katin shaidan aikin Dan sanda na bogi wajen karbar kudi da kuma musgunawa jama’a da ba su ji ba ba su gani ba, wanda hakan ya jawo bata wa rundunar suna, inda ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Olatoye Durosinmi ya gargadi masu kwaikwayi ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro cewa, su daina kai tsaye ko kuma su fuskanci fihsin rundunar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, abubuwan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da katin shaidar dan sanda na bogi da kuma wani adadi mai yawa na tabar wi-wi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za Mu Yi Magana Da Yan ta’adda Da Yaren Da Suke Fahimta—-Buhari
Sanarwar ta cigaba da cewa, “Jami’an rundunar yan sandan jihar sun kama wani Vincent Sampson Enuneku mai shekaru 43 dan asalin karamar hukumar Ndokwa ta jihar Delta bisa zarginsa da aikata wani abu mai girma.
An kama wanda ake zargin ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2022 a Uyo yayin da yake kokarin yin amfani da katin shaidar aikin dan sanda mai mukamin mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) na bogi don hana kama wani mai laifin da ake nema ruwa a jallo.”
A WANI LABARIN KUMA: Matsalar Tsaro: Idan Na Sauka A Mulki, Mutanen Jihar Kogi Zasu Yi Kewa Na– Gwamna Bello
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tabbatar da cewa za a yi kewar sa wajen sadaukarwar da ya bayar musamman dangane da kashe kudade kan harkokin tsaro a kokarinsa na ganin ‘yan jihar sun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan wa’adinsa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake magana a wani shirin Breakfast na Gidan Talabijin na kasa Najeriya wato NTA, inda aka tattaunawa game da ayyukan Gwamnoni a harkar tsaron kasa.