By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta cafke wasu mutane biyar da ake zargi da satar babura a Ikirun, Iragbiji da Osogbo, babban birnin jihar.
Wadanda ake zargin sun hada da James-Oke Oladele, Hamsat Jamiu, Abayomi Atanda, Akanji Samuel da Kazeem Onaopepo.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Olokode, ya gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda da ke Osogbo.
Ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin sun kai hari ne kan wani direban babur inda suka kwace babur dinsa a unguwar garejin Ilesa a Osogbo.
CP ya ce kama wanda ake zargi na farko ya sa aka kama wasu da ake zargi a Ikirun da Iragbiji bi da bi.
Wadanda ake zargin sun amsa cewa sun kwace babura da dama a wurare daban-daban tare da sayar da su.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce an kwato baburan kirar Bajaj guda biyu daga hannun wadanda ake zargin, ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin kwato karin baburan da aka sace daga hannun wadanda ake zargin.
Olokode ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a hannu a cikin lamarin.