‘
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta ce ta kama wasu mutane 18 da ake zargin barayin shanu ne, wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shanu da sauran dabbobin gida daga jihohin Bauchi, Filato da Taraba.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai a jiya, kwamishinan ‘yan sanda, Ishola Babaita, ya ce kungiyoyin ‘yan sanda tare da hadin gwiwar kungiyoyin ‘yan banga da mafarauta ne suka hada hannu tare da bin diddigin ‘yan fashin bayan da aka samu labarin.
Ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a kusa da mahadar Kalmai na karamar hukumar Billiri a jihar.
A cewarsa, da ganin jami’an tsaron, barayin sun watsar da dabbobin suka gudu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba A Kore Ni Daga Takarar Sanatan Ebonyi Ta Kudu Ba – Umahi
Sai dai ya ce ‘yan sandan sun samu nasarar cafke 18 daga cikinsu, wadanda ya ce suna taimaka wa ‘yan sanda da bayanai.
Babaita ya bayyana cewa an kwato shanu 483, tumaki da raguna 186, jakuna uku, babura hudu, wayoyin hannu tara, da kudi Naira 994,000 daga hannun wadanda ake zargin.
Ya kuma bayyana cewa, abubuwan da aka kwato sun hada da bindigogin kirar AK-47 guda biyu, bindigu AK-49 daya, harsashi guda 320, kundun alburusai 14 da babu komai a ciki, da kuma alluran maye guda uku.
A wani labarin kuma na daban,
A kalla jam’iyyu 18 ne za su fafata a zaben gwamna a jihar Sakkwato, kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana a ofishinta da ke Sokoto.
A karon farko Jam’iyyu guda biyu sun sanya ƴan takarar mataimakan Gwamna mata.
Sun hada da Hannatu Muhtar wadda ita ce mataimakiyar ‘yar takarar gwamna a dandalin jam’iyyar Action Peoples Party da Hauwa’u Bello wadda ita ce mataimakiyar ta Jam’iyyar Allied Peoples Movement.
A yayin da wakilinmu ya ziyarci ofishin INEC, baya ga ’yan takarar jam’iyyar All Progressive Congress and Peoples Democratic Party, suna da Saidu Umar da Ahmed Aliyu Sokoto.
Sauran sun hada da Isiyaku Bello na ADC, Abubakar Haruna na APM, Habibu Muhammed na Zenith Party, Ibrahim Muhammed Mansur Gada APGA da Goronyo Ibrahim na Boot Party.
Akwai kuma Dahiru Umar Tambuwal na NNPP, Muhammad Saidu Gumburawa na PRP, Daniya Usama Sani na YPP, Imam Abdulrahim Chindo na Labour Party yayin da National Rescue Movement ta gabatar da Aliyu Sulaiman DanDauda.
Action Alliance ta gabatar da Ahmad Ahmad Jao, ADP na da Nasiru Sarki Larabawa, SDP na da Umar Abdul-Razak, African Action Congress tare da Ahmad Babajo Ibrahim da Abba Sidi Ahmed ga Jam’iyyar Action Peoples Party.