Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta ce ta ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Ajaokuta zuwa Itobe a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP William Aya, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya Litinin a Lokoja, babban birnin jihar.
Ya ce an kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su ne bayan da jami’an ‘yan sanda suka tarwatsa gungun ‘yan bindiga da suka addabi masu ababen hawa a kan hanyar.
“A ranar 18 ga watan Disamba, 2021, da misalin karfe 4 na yammaci, mun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar da ke tsakanin NEPA da ASCOL a kan hanyar Itobe zuwa Ajaokuta, suna harbi lokaci-lokaci don tsoratar da masu ababen hawa, Inda su aikata mugun aikin.
“Ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sandan suka dura zuwa wurin da lamarin ya faru, suka kama ‘yan ta’addan amma wasu sun tsere cikin daji kuma ana cikin haka ne suka kubutar da mutane biyu daga hannun Yan bindiga ba tare da wani rauni ba. Ana ci gaba da kokarin ganin an kama sauran ‘yan bindigar,” in ji shi.
A wani labarin kuma, jami’an ‘yan sandan da ke aiki da sashin Enjema a jihar Kogi ta Gabas sun cafke wasu mutane biyu Mohammed Alhaji da Amadu Sule Juji, wadanda suka kware wajen satar shanu.
“Ba tare da bata lokaci ba rundunar ‘yan sandan ta dauki matakin ta hanyar gudanar da bincike tare da kama wadanda ake zargin a Ogboji da ke Unguwar Ankpa tare da kwato shanu 14.
“Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike,” in ji Aya
Comments 2