Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata laifuka, bayan ta kai samame kan maboyar ‘yan ta’adda a kananan hukumomin Birnin Kudu da Gwaram na jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN hakan, a garin Dutse ranar Talata.
Shiisu ya ce uku daga cikin wadanda ake zargin, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 28, an kama su ne a kauyen Babaldu da ke karamar hukumar Birnin Kudu, a lokacin da tawagar ‘yan sanda da ke sintiri suka kai samame maboyar masu aikata laifuka a yankin.
PPRO ya kara da cewa an samu daya daga cikin wadanda ake zargin yana da alaka da laifin kisan kai da ya faru a watan Agustan 2021.
Idan za’a tuna cewa, a ranar 6 ga watan Agusta da misalin karfe 7:50 ne wasu fusatattun mutanen kauyen (Babaldu) suka fatattaki wani da ake zargin barawon babur ne suka kashe shi tare da kona shi.
Ya ce sauran mutane hudun da ake zargin an kama su ne a garin Sabuwar Gwaram da ke karamar hukumar Gwaram, a lokacin da ‘yan sanda suka kai samame a wani wuri da ake zargin maboyar su ne a yankin.
Ya ce wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 20 zuwa 40, an kama su ne da robar Sholi guda hudu a hannunsu.
PPRO ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike bayan an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu. (NAN)