By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara a ranar Juma’ar da ta gabata ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne ta kan iyaka, Mohammed Alo, a wani dajin da ke Kosubosu, hedikwatar karamar hukumar Baruten ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce an kwato kudi naira miliyan 2.3m daga hannun dan kasar Benin.
Ya kuma kara da cewa jami’an tsaro sun kwato bindigar gida, wuka, adduna daya da wayoyi biyu daga hannun wanda ake zargin.
Okasanmi ya ce, “Tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na sashin Kosubosu, tare da taimakon ‘yan banga, sun afka cikin dajin da ke cikin Kosubosu a yankin Baruten, inda suke neman wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke kutsawa cikin dajin.
“Saboda haka, binciken kwakwaf da ‘yan sanda da ‘yan banga suka yi a cikin daji ya kai ga kama wani Mohammed Alo, dan jamhuriyar Benin.
“An karbo wasu abubuwa daga hannun sa sun hada da bindiga guda daya da aka yi a gida, adda daya, wuka guda daya, wayoyin hannu guda biyu na model daban-daban, Bluetooth daya da kudi Naira miliyan 2,300,000.
“Wanda ake zargin ya amsa cewa shi mamba ne na kungiyar masu garkuwa da mutane ta kan iyaka, wadanda sauran ‘yan kungiyar su ke a Jamhuriyar Benin.
“Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.”