Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta cafke kwamandan ‘yan banga na jihar Anambra da laifin azabtar da wata ‘yar sanda a ranar 12 ga watan Janairun 2022.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Ikenga Tochukwun ne, ya tabbatar da kamen a Awka ranar Asabar.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Echeng Echeng, ya bayar da umarnin kama wanda ake zargin, wanda ba a ambaci sunansa ba, biyo bayan rahoton cin zarafi da azabtarwa da aka yi wa wata ‘yar sanda a ofishin tsaro na AVG na garin Awuda Nnobi.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa rundunar a shirye take ta kare mata daga cin zarafi ko da kuwa wacce ba ta daya daga cikin cikin jami’an tsaro.
Ya godewa al’umma musamman na Ndi Anambra bisa yadda suka suka yi Allah wadai da wannan aiki da kuma kare jinsin mata.
Ya ce, “Bayan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda aka ga wasu ‘yan kungiyar Vigilante ta Anambra suna cin zarafin wata mata a ofishinsu da ke Awuda Nnobi. CP ya ba da umarnin a kamo kwamandan nan take kuma tuni aka fara bincike.
“Rundunar, a yau, tana so ta sanar da jama’a, musamman na garin Ndi Anambra cewa, an kama kwamandan AVG da laifin azabtar da wata ‘yar sanda a ranar 12 ga Janairu 2022 a ofishin tsaro na Awuda Nnobi kuma yana hannunmu.” Inji sanarwar.