By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama Marshal Abubakar, lauyan dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore.
Marshal lauya ne wanda ya kasance yana aiki a Femi Falana Chambers a Abuja.
Dan gwagwarmayar ya bayyana haka ne ta shafinsa na Facebook a ranar Juma’a.
A cewar mawallafin Sahara Reporters, an kama Abubakar da karfi.
“An bi sahun Marshal DF Abubakar zuwa gidansa kuma aka kama shi da karfi saboda an zarge shi da kare ni.
“Sun yi ikirarin cewa ya kunyata ‘yan sanda ta hanyar kai su kara da Ned Nwoko a madadina,” in ji shi.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya a baya ta bayar da rahoton kama Sowore tare da tsare shi a ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairu a Abuja bayan wani dan majalisar wakilai kuma dan kasuwa, Prince Ned Nwoko ya shigar da kara.
Sai dai kuma daga baya aka sake shi a daren ranar Alhamis.
Nwoko ya kai karar rundunar ‘yan sandan Najeriya a kan Sowore da laifin bata sunan sa, munanan labaran karya da aka sani da ya sabawa sashe na 391, 392, 393, 394, 395, da 418 na kundin laifuka na Arewacin Najeriya.