By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mafarauta guda uku da wasu da ake zargi da hada baki wajen taimakawa masu garkuwa da mutane a kananan hukumomin Girei da Fufore a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sulaan Nguroje, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce wadanda ake zargin: Auwal Mohammed mai shekaru (28), Isa Umaru (40), da Rabiu Mohammed (19) sun addabi kauyukan Pariya Daware da Girei.
Ya ce rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kwato babur daya, bindigogin gida da sauran kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin.
“Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa wadanda ake zargin sun ci amanar amincewar al’umma da aka ba su na kare rayuka da dukiyoyi, sun ci gaba da samar da kayayyakin abinci da sauran bukatun yau da kullum ga ‘yan uwansu masu garkuwa da mutane a kewayen yankin,” in ji sanarwar.
Kazalika yace ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin kuma za’a gurfanar dasu a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
A WANI LABARIN KUMA
Wasu mata biyu ne suka rasa rayukansu sannan sama da gidaje 30 ne aka ce sun ruguza sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Asabar a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
A cewar wani jami’in yada labarai na karamar hukumar Abdulkarim Sani, daya daga cikin matan ta mutu ne bayan da bangon ginin nata ya ruguje ya fado mata. ya ce tun a lokacin an binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sani ya kuma bayyana cewa, al’ummar Nasarawa da Matsiga ne suka fi fama da bala’in ruwan sama da ya afku a tsakanin daran ranar Asabar da Lahadi.
Hukumomin yankin na ci gaba da kokarin tantance yawan barnar da ruwan yi wa mutane, gidaje da gonaki kamar yyaadda rahotonni suka bayyana.
Har yanzu dai Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ba ta fitar da wata sanarwa ko amsa tambayoyi kan lamarin ba
Comments 1