Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama tare da tsare shugaban jami’ar Oduduwa, Ipetumodu (OUI), Dokta Ramon Adegoke Adedoyin da wasu mutane shida bisa zargin kashe wani dalibin jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife na jihar Osun, Mai suna Timothy Adegoke.
Adegoke wanda dalibin digiri ne a mataki na biyu a Jami’ar OAU ya zo Ile-Ife daga Abuja domin zana jarabawarsa a sashin koyo daga gida na jami’ar OAU, Moro, jihar Osun.
Duk da haka, ba a san inda yake ba bayan jarrabawar kuma an bayyana bacewarsa a ranar 7 ga Nuwamba shekarar 2021.
Da yake magana a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Olokode a ranar Laraba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da cewa Adedoyin wanda fitaccen dan kasuwa ne a Ile-Ife yana cikin ofishin ‘yan sanda, akan rasuwar Adegoke.
“Baya ga wadanda ake zargi shida da aka kama a baya, an kuma kama shugaban otal din Hilton da Resort dake garin Ile-Ife, Dokta Ramon Adegoke Atobatele Adedoyin. Yanzu haka yana tsare a hannun ‘yan sanda, inda ake yi masa tambayoyi dangane da lamarin, yayin da yake jiran rahoton binciken gawar daga asibiti.” Inji shi.
Comments 1