Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane uku da suka yi yunkurin yin sata a babban kanti na NEXT Cash and Carry a lokacin da wuta ta tashi a safiyar jiya Lahadi.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a yanar gizo, an ga wasu mutane na tura keken dakon kaya da suka yi amfani da su wajen kwashe abubuwan da ake zargin an sace.
Sai dai a wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta fitar ta bakin kakakinta, Josephine Adeh, ta ce babu wani nasarar da aka samu na sace-sacen manyan kaya a kantin.
Adeh ta bayyana cewa jami’an tsaro yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kai dauki cikin gaggawa domin kashe gobarar da kuma hana sace-sacen manyan Kayayyaki a kantin.
Ta kuma ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.
Kazalika Kakakin ‘yan sandan ta bayyana wadanda aka kama kamar haka: Ali Audu, mai shekaru 18; Yahaya Yunusa mai shekaru 20 da kuma Sahabi Abubakar mai shekaru 20.