Rundunar ‘yan sandan jihar Borno a ranar Litinin ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata fyade da kuma wata mata dauke da sinkin harsashi 90.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Abdu Umar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Maiduguri, inda ya ce an kama wasu mutane 52 bisa laifuka daban-daban a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin Abubakar Baba mai unguwar Gwange da ke Maiduguri ya yi wa yara hudu fyade ‘yan shekara hudu zuwa bakwai.
“Wani wanda ake zargin, Bilyaminu da ake yi wa lakabi da Mallam Sale na garin Gwange ya yaudari wata yarinya ‘yar shekara shida mai da take Unguwar, zuwa cikin wani Masallaci da karfin tsiya inda Kuma yayi lalata da ita.
“Har ila yau, akwai wata Anita Yusuf da ke kauyen Wamdeo a karamar hukumar Askira/Uba da aka kama da harsashi AK 47 har guda 90 kuma yanzu haka tana baiwa ‘yan sanda bayanai masu amfani,” in ji Umar.
Sauran wadanda ake zargin sun hada da wasu mutane takwas da aka kama da laifin lalata da satar igiyoyin wutar lantarki a garin Bama, da kuma wasu 25 da aka kama da laifin tada hankalin jama’a, a taro ba bisa ka’ida ba, da kuma mallakar muggan makamai da miyagun kwayoyi.
Shugaban ‘yan sandan ya ce za a gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a gaban kotu bayan an kammala bincike.
Umar ya bukaci kafafen yada labarai da su bi diddigin lamarin don kammalawa.
Da yake magana da manema labarai, Yusuf ya ce, alburusan da aka samu a hannunta, ta ce saurayin ta, soja ne ya ba ta, domin ta kai wa direban da zai kai wa wani soja a Yola.
Yusuf ya yi ikirarin cewa ba ta da masaniya cewa kayan da aka ba ta a cikin jakar Leda na polythene harsashi ne.