Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata laifin kisan kai ta hanyar Asiri, a sassa daban-daban na babban birnin Abeokuta.
Wadanda ake zargin sun hada da Lekan Oladipupo (38), Sulaiman Aremu (30), Ifayemi Madru (24), Shittu Saheed (38), Samod Sulaiman (35), Akanji Moruf (23) da Tajudeen Adekunle mai shekaru 36.
An kama su ne biyo bayan rahoton da wani Abraham Okosun ya kai hedkwatar rundunar Yan sanda dake Bode Olude.
Wanda ya shigar da karar ya shaidawa ‘yan sanda cewa ya ziyarci dan’uwansa mai suna Sunday Okosun a kauyen Agbara ta Mawuko Abeokuta, sai dai ya gano cewa an yi wa dan’uwan kisan gilla tare da tarwatsa gawarsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa manema labarai a Abeokuta cewa, bayan rahoton, DPOn yankin Bode Olude, DSP Durojaye Rotimi, ya jagoranci tawagar jami’an sa zuwa wurin.
A cewarsa, rundunar a lokacin da take aiki da sahihan bayanai, ta gano tare da cafke Lekan Oladipupo, wanda a yayin da ake yi masa tambayoyi ya bayyana cewa shi ne ainihin wanda ya harbe marigayin da bindigar sa ta Dan-Dane.
Oyeyemi ya ce furucin da ya yi ne ya sa aka damke sauran mutane shidan da ake zargi.
Ya ce yayin da ake gudanar da tambayoyi daban-daban, kowanne daga cikin wadanda ake zargin “ya bayyana irin rawar da ya taka a cikin mummunan kisan da aka yi wa marigayin da kuma wasu da aka kashe a irin wannan yanayi.”