By Abbas Yakubu Yaura
Rikici ya dabaibaye shinkafar da kuma kyautar Kirsimeti na naira 500,000 da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya baiwa mabiyansa a karamar hukumar Ijebu ta Arewa.
An kama mutane uku tare da tsare su bisa laifin zamba da kyaututtukan.
Sai dai wani lauya, A.D. Sosanwo, ya bukaci hukumar ‘yan sanda ta yankin Ijebu Ode ta biya naira miliyan 10m saboda tsare mutane uku da ya bayyana a matsayin abokan huldarsa ba bisa ka’ida ba.
Sosanwo, a cikin takardar koke ga ‘yan sanda wanda aka aika kwafin zuwa ga Sufeto-Janar na ‘yan sanda dana Jihar Ogun.
Kwamishinan ‘yan sandan, ya bayyana cewa an kama wadanda yake karewa ne a ranakun 2 da 3 ga watan Janairu, 2022 kuma ana tsare da su fiye da takamaiman lokacin da tsarin mulki ya kayyade.
Ya bayyana sunayen wadanda ake tsare da su Morufu Idowu, Adebayo Rabiu da Wasiu Raji, inda ya kara da cewa an kama su ne bisa umarnin sakataren gwamnatin jihar, Mista Tokunbo Talabi.
A cewar koken, jami’an ‘yan sanda sun kama mutanen ne a Ago-Iwoye tare da mika su ga rundunar ‘yan sandan yankin Ijebu-Ode.
An zarge su da daukar wasu buhunan shinkafa da ake son rabawa al’umma.
Lauyan ya bayyana cewa Kwamandan yankin ya bukaci a mayar da buhunan shinkafar inda za a warware matsalar cikin ruwan sanyi.