Yan sanda a jihar Zamfara sun kame daya daga cikin yaran fitacen dan bindiginan da ke satar shanu Bello Turji, a wani samame da suka kai a maboyarsu dake kusa da garin Gumi na jihar ta Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar “yan sanda ta jihar SP Muhammad Shehu ne ya tabbatarda hakan.
Ya ce nasarar kame dan bindigar, mai suna Abdullahi Umar wanda aka fi sani da Sangamere ya biyo bayan wani rahoton sace wata mata da rundunar ta samu mai suna Hajiya Inno mai kimanin shekaru 60 yar garin Gambanda A Magero dake karamar hukumar Gumi a ranar 21 ga watan Maris din shekarar 2022 wanda ake zargin yan bindigar da aikatawa.
Da ga nan ne rundunar yan sanda ta fara gudanar da bincike wanda yayi sanadiyar kame mutum 8 da ake zargin yan bindiga ne ciki harda daya daga cikin kwamandodin na Bello Turji.
Yan bindigar da ake zargi tare da wadanada ke taimaka musu sun da de suna addabar garin Gumi da sauran yankunan da ke yankin.
To sai dai yanzu suna hannu yan sanda inda suke fuskantar bincike mai tsanani, domin samun damar kama sauran gungun yan ta addar domin mika su ga hukuma ta hukun tasu.
SP Shehu yace bayan sunyi ma matar da aka ceto gwage- gwage lafiya , tuni suka mika ta ga iyalanta.
Hakanan kuma jami’yan yan sandan sun dakile wasu hare hare daga yan bindigar a garuruwan Kwaren Ganuwa, da Nasarawar Mai fara a karamar hukumar tsafe a jihar ta zamfara.
Inda a wurin fafatawar suka kame wani dan bindiga guda daya, sun kuma yi nasarar kwato bindiga kirar AK47 da mashin daga hannun yan bindigar.
Rundunar ‘yan sandan ta jihar Zamfara karkashin jagoranci CP Ayuba .Elkanah ta bukaci al’ummar da ke jihar da su taimaki rundunar da sauran jami’yan tsaro a yakin da su keyi da Yan bindiga, kuma su taimake su da addu’oi domin samun zaman lafiya a jiha Zamfara da ma kasa baki daya.
Awani labari kuma Duk dai akan sha’anin tsaron Jami’yan ‘yan sanda sun damke wasu mutum uku da suka hada da wani soji da ake zargi da sace wata dalibar jami’a a jihar Ekiti.
Kazalika yayin wannan yunkurin jami’an tsaron sun ceto dalibar daga hannun masu Garkuwan.
An dai kame mutane a dakinsu na wani otel dake Ado-Ekiti babban Birnin Jihar.