Rundunar yan sanda a jihar Ekiti ta ce, ta kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a garkuwa da wasu ma’aurata.
An yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Ilasa zuwa Ayebode, da ke karamar hukumar Ekiti ta Gabas, da yammacin jiya Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa, Ma’auratan na dawo wa ne daga Ado Ekiti, inda suka je siyan kayayyaki a shirye -shiryen daurin auren su.
Daga baya masu garkuwa da mutanen sun tuntubi danginsu, inda suka nemi Naira Milliyan 5 a matsayin kudin fansa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Kungiyoyin sun nuna goyan bayan su Obibanjo
Kakakin rundunar yan sandan jihar, ASP Sunday Abutu ya tabbatar da cafke mutane ukun da ake zargi da hannu a garkuwa da Ma’auratan.
A wani labarin Kuma na daban
Wasu mazauna Unguwar Rijiya Biyu, dake Jakara a jihar Kano a ranar Litinin sun shiga cikin rudani yayin da wani uba mai suna Lawal Bello, dan shekara 35, ya lakadawa dansa mai suna Abubakar Abba, dan shekara 10 dukan kawo wuka.
Rahotonni sun bayyana cewa Bello ya yi wa dan nasa dukan tsiya saboda taurin kai kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya ce‘ yan sanda sun yi nasarar cafke mahaifin da ya gudu bayan mummunan lamarin, ya kara da cewa “mun samu rahoto da misalin karfe 7 na safe daga Unguwar Rijiya Biyu da ke unguwar Jakara a Kano inda wani uba, Lawal Bello, dan shekara 35 ya buge dansa, Abubakar Abba, dan shekara 10 har lahira.
Da samun rahoton, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Sumaila Dikko ya tura mutanensa da jami’in da suka shiga aiki suka ziyarci inda abin ya faru inda suka dauki marigayin zuwa asibitin Murtala inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
“Mahaifin da mahaifiyar duka sun tsere daga wurin bayan faruwar lamarin amma daga baya an cafke mahaifin kuma yanzu haka yana hannun‘ yan sanda inda tuni mahaifin ya furta cewa ya aikata laifin.
“Kwamishinan‘ yan sandan ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin, Sai dai kuma rundunar ‘yan sandan ta gargadi iyaye da sauran mazauna yankin da su guji daukar doka a hannunsu,” inji DSP Haruna.
Mahaifin marigayin, Bello, duk da haka ya ce ya nemi taimakon yaran don samun ruhaniya amma babu wani canji saboda haka bugun ya kai ga mutuwarsa.