Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo sun cafke wani matashi dan shekara 21 mazaunin Kano, Mai suna Yakubu Idris, bisa zargin barazanar yin garkuwa da shugaban kungiyar Hausawa a birnin Benin, Alhaji Badamasi Saleh.
An kama wanda ake zargin ne biyo bayan korafin da Alhaji Badamasi Saleh ya yi kan barazanar da wani da ba a san ko wanene ba ya yi na yin garkuwa da shi.
An tattaro cewa a ranar 16 ga watan Satumba, Saleh ya kai karar kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo cewa, wani da ba a san ko wanene ba wanda ya yi ikirarin cewa shi dan kungiyar masu garkuwa da mutane ne da ke zaune a Birnin-Gwari a jihar Kaduna, ya yi barazanar yin garkuwa da shi.
Wanda ake zargin ya shaida wa Saleh cewa wani na kusa da shi (Saleh) ya biya shi Naira miliyan daya domin ya yi garkuwa da shi amma ya yanke shawarar bayyana masa shirin domin shi mutumin kirki ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: An tsige Kakakin Majalissar Dokokin Filato
An ce wanda ake zargin ya dage cewa dole ne Saleh ya biya Naira miliyan 1 a cikin wani bankin GT da aka kebe domin kwantar da hankalin ‘yan kungiyarsa don kada su aiwatar da shirin yin garkuwa da su.
An kuma ruwaito cewa ‘yan sandan sun bukaci Saleh da ya yi wasa tare da tattaunawa da wanda ake zargin wanda aka kama bayan an biya kudin a asusun bankin da ya bayar.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar, Kontongs Bello, ya tabbatar da kama shi.
Ya ce an bukaci wanda ya shigar da karar ya tattauna da wanda ake zargin ya karbi Naira 100,000 da aka biya a asusun sa na bankin GT.
Ya ce a lokacin da aka samu bayanan an biya kudaden a cikin asusun; ‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargin a maboyar sa da ke jihar Kano.
Kontongs ya kara da cewa, a yayin binciken an gano cewa, wanda ake zargin wani ne wanda mai karar ya taimaka mawa a baya lokacin da yake kasar Benin.