Wani matashi dan shekara 22 a unguwar Oke-Gada da ke karamar hukumar Ede na jihar Osun, Toluwalope Oladoye, ya shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 16.
An tsare shi ne a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ede, inda daga bisani aka mayar da karar zuwa sashin kare marasa galihu da kuma banbancin jinsi da ke ofishin ‘yan sanda na Osogbo, babban birnin jihar.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.
A halin da ake ciki, Asusun Kula da Yawan Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA), tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta, Action Health Incorporated (AHI), na kara gudanar da gaggamin wayar da Kai a jihar don karfafa matakan shari’a game da cin zarafin mata da kananan yara.