‘Yan sanda sun cafke daya daga cikin jagororin’ yan Biafra (IPOB), Uchenna Chukwu, a jihar Imo
Kakakin ‘yan sanda a jihar, CSP Mike Abatta a cikin wata sanarwa da ya fitar a Owerri a yau Juma’a ya ce, an damke dan IPOB din ne , a karamar hukumar Ehime-Mbano da ke jihar.
Ya kara da cewa ‘yan sanda sun kuma kashe wani dan kungiyar IPOB wanda ya hada kai da sauran membobin don dakile yunkurin jami’ai na kama Jagoran.
Ya ce, Chukwu, mai shekara 34, ya taka rawa sosai wajen kashe jami’an ‘yan sanda da dama da kona ofisoshin‘ yan sanda a Imo, kuma an dade da bayyana cewa, ‘yan sanda suna nemansa.
KARANTA WANANN LABARIN: Harin Bam ya kashe yan shi’a 50 a Afghanistan
Ya bayyana cewa, sakamakon samun sahihan bayanai, ‘yan sanda sun mamaye shagonsa da ke yankin Ehime Mbano don kama jagoran.
Ya kara da cewa, an Sami bindiga guda biyu da aka kerar cikin gida, tare kwato harsasai guda biyu.
Abattam ya kuma bayyana cewa, wanda ake zargin a halin yanzu yana amsatambayoyi, kuma ya yiwa ‘yan sanda bayani.
Kazalika Ya ce ‘yan sanda na aiki tare da sauran hukumomin tsaro don cafke sauran’ yan kungiyar ta’addanci musamman wadanda suka tsere da raunin harsashi.