Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke wani da ake zargi da Mai garkuwa da mutane a kauyen Soro Daya da ke karamar hukumar Tsanyawa na jihar.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar PPRO, Mista Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar jiya a Garin Kano kuma Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta samu ya ce, an shigar wa da rundunar korafi a ranar 1 ga Satumba shekarar 2021, daga wani mazaunin Danzabuwa a wani kauye na karamar hukumar Bichi a jihar, inda a ke yi masa barazana ta wayar tarho cewa, zai biya Naira miliyan daya in ba haka ba za a yi garkuwa shi ko daya daga cikin yaransa.
“Bayan karbar korafin da rundunar ta yi , Kwamishinan yan sandan reshen jihar Kano, Sama’ila Dikko, ya umurci tawagar jami’an binciken Sirri, karkashin jagorancin SP Shehu Dahiru, da su gano tare da cafke mai amfani da layin wayan ”
“ Hakan yasa tawagar fara bin diddigin Layin wayar inda rundunar ta gano tare da cafke wanda ake zargi Mai suna Tukur Ahmad Mai shekaru 28, wanda ya fito daga kauyen Soro Daya na karamar hukumar Tsanyawa na jihar Kano, a Kauyen Panda, dake Karamar hukumar Keffi na Jihar Nassarawa, a ranar 25 ga watan Satumban shekarar nan, ”in ji Haruna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kuto ta dakatar da Shari’ar Tsohon Gwamnan Abia Kanu
Kazalika ya ce, lokacin binciken farko, wanda ake zargin ya bayyana cewa, shi dangin mai karar ne, kuma ya amsa laifin da ake zargin sa dashi, inda ya kara da cewa, nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wanda ake zargi zuwa kotu da zaran an kammala gudanar da bincike.
Kwamishinan ya kuma ya Bawa jama’ar jihar Kano baki daya, bisa hadin kai da goyon baya da suke ba su, sannan ya bukace su, da su ci gaba da kai rahoton wadanda ake zargi da laifi zuwa ofishin yan sanda mafi kusa da su, don daukar matakin gaggawa.