Yan sanda sun kama wani likitan jabu bayan shafe watanni 10 yana aiki
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani likitan jabu wanda har yanzu ba’a tantance ba wanda ke aiki tun watan Janairun 2022.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, wanda ya bayyana hakan a wani sakon Twitter a ranar Asabar, ya ce wanda ake zargin yayi karyar takardar shaidar likita da sunansa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kana Ɗaya daga cikin ginshikan cigaban Kiristanci a Najeriya — Buhari ya taya sabon shugaban Kiristoci Murna
A cewarsa, wasu mazauna jihar ne suka hango wanda ake zargin kuma suka mikawa rundunar bayanan.
Da take raba hoton wanda ake zargin, PPRO ta rubuta: “Wannan mutumin mai shekaru 26 ya karya lasisin likita da sunansa kuma yana aikin likita tun watan Janairu 2022.
“Yabo ya tabbata ga ’yan Legas masu son jama’a da suka gan shi kuma suka sanar da ‘yan sanda ba tare da bata lokaci ba. Kun ceci rayuka. Idan kun ga wani abu, ku faɗi wani abu
A wani labarin kuma: 2023: Wike zai ƙare a gidan yari – Ned Nwoko
Yakin baki tsakanin Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da Sanata Ned Nwoko ya dauki wani salo.
Wike ya yi a cikin wani faifan bidiyo da nufin tono Nwoko kan dala $418 na Paris Club.