Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Asabar din da ta gabata ta kama wani matashi mai shekaru 33 da haihuwa mai suna Agbo Victor, da take zargi mai fataucin miyagun kwayoyi ne, dauke da fakiti 250 na tabar wiwi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.
Haruna-Kiyawa ya ce jami’an rundunar ‘yan sandan sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake tafiya a cikin wata mota makare da Tabar Wiwin a Kwanar Dangora dake karamar hukumar Kiru ta jihar Kano.
Haruna-Kiyawa ya ce wanda ake zargin ya yi jigilar kayan ne daga jihar Edo zuwa wani dillalin kwayoyi a Kano, wanda yanzu haka ya kama.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Samaila Shuaibu-Dikko, ya bayar da umarnin mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar, sashin binciken miyagun kwayoyi domin gudanar da bincike mai zurfi.
Kakakin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Da yake nanata kudurin hukumar na kawar da miyagun ayyuka, Haruna-Kyawa ya bukaci jama’a da su rika baiwa ‘yan sanda sahihin bayanai kan masu kai-kawo a cikin al’ummarsu.
A wani labarin kuma na daban
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya tallafawa marayu 200 daga sassa daban daban na kananan hukumomi 17 na jihar da kudi naira 50,000 kowannen su.
Buni ya ce an yi hakan ne don a taimaka musu da dan jarin fara sana’a bayan samun kwarewa.
“Fatan mu ne cewa wannan taimakon zai karawa rayuwarku zuwa gaba wajen rike kawunan ku,” in ji gwamnan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shekarun marayun sun kasance daga shekara 9 zuwa 14.
Ustaz Babagana Malam Kyari, babban jami’in shirin kuma mai ba Gwamna Buni shawara kan harkokin addini, ya ce wannan shi ne karon farko da aka tallafa wa marayu da yawa a fadin jihar.
Ya ce hakan zai rage ya waitar karuwar barace-barace a kan tituna, musamman marayun da ba su da sana’ar yi.
Kyari ya yi kira ga masu kula da marayun da su tallafa musu tare da tabbatar da yin amfani da kayan a bisa gaskiya da rikon amana.