By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun tace ta kama wani fitaccen otaldin shakatawa dake Ile-Ife (wanda aka sakaya sunansa) bisa mutuwar dalibin digiri na biyu na Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU).
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Osun SP Yemisi Opalola, ya fitar a Osogbo, tace an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin, kuma yanzu haka ana yi masa tambayoyi.
Opalola yace ma’aikacin otal din shi ne na baya-bayan nan da aka kama dangane da lamarin, inda yace tun da farko an kama mutum shida.
“An kama su ne dangane da mutuwar Mista Timothy Adegoke, dalibin Digiri na biyu a jami’ar OAU, wanda ya zo daga Abuja domin zana jarrabawar sa a Cibiyar Koyon Nesa ta OAU, Moro, Osun,” inji shi.
A cewarsa, kwamishinan ‘yan sanda, Olawale Olokode, na fatan sanar da jama’a cewa, baya ga wadanda ake zargi mutane shidan da aka kama a baya, an kuma kama mai otal din a ranar 15 ga watan Nuwamba.
“Yanzu haka yana tsare a hannun ‘yan sanda, inda ake yi masa tambayoyi dangane da lamarin, yayin da yake jiran rahoton binciken gawar asibitin,” in ji Opalola.
Ya godewa jama’a musamman ‘yan uwa da dalibai da kuma jami’an hukumar jami’ar ta OAU bisa hadin kan Da suka ba ‘yan sanda su ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
“Kwamitin CP ya sake nanata kudurin rundunar ‘yan sandan jihar na tabbatar da cewa an yi adalci ko ta wanne hali.
Kazalika An kuma bayyana cewa marigayin ya sauka a wani otal da ke Ile-Ife, sau da dama tsakanin 22 ga watan Oktoba zuwa 5 ga watan Nuwamba, inda aka bayyana cewa ba a ganshi ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wata sanarwa da ofishin hulda da jama’a na jami’ar, Mista Abiodun Olanrewaju, ya fitar, tace mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da takaici.
“Mataimakin shugaban jami’ar ya yi alkawarin yin aiki tare da jami’an tsaro domin bankado al’amuran da suka kai ga mutuwar Mista Adegoke.
Comments 1