Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta kama wasu matasa biyu bisa zargin laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade a Rumudomaya da ke karamar hukumar Obio Akpor na jihar.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, an kama wadanda ake zargin, Chibuike Mai shekara (15) da Christopher (14) a ranar Litinin, yayin da ake tsare da mutum na uku.
Mahaifin yarinyar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, a watan Nuwamba shekarar 2021, yaran uku sun yi awon gaba da ‘yarsa a unguwar Rumudomaya a kan hanyarta ta zubar da shara da misalin karfe 7:00 na dare, inda suka kai ta wani waje, suka yi lalata da ita kuma suka tsare ta a wurin na wajan sama da sa’o’i uku”
Sashen hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da kamen wadanda ake zargi.