Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da gudanar da wata haramtacciyar kwalejin kimiyyar lafiya a karamar hukumar Bosso ta jihar.
DSP Wasiu Abiodun, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Talata a Minna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Inganta Wutar Lantarki A Najeriya – Adesina
Abiodun ya ce mutanen biyu da ake zargin sun fito ne a matsayin mai gida da kuma daraktan kwalejin kimiyyar kiwon lafiya ta haramtacciyar hanya da ke Maikunkele a karamar hukumar Bosso, sun fito ne daga karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da kuma jihar Enugu.
PPRO ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 9 ga watan Satumba, bisa bayanan sirri da sashen leken asiri na rundunar ya samu.
“An zargi mutanen biyu da kafawa da kuma gudanar da makarantar bogi da aka fi sani da Excellence College of Health Sciences and Technology, dake unguwar Maikunkele a karamar hukumar Bosso.”
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargi da mallakar makarantar ya amsa cewa ya kafa makarantar a shekarar 2020 kuma ya fara daukar dalibai a makarantar a shekarar 2021 ba tare da neman izini ko takaddun shaida daga hukumomin gwamnati da suka dace ba.”
“Ya kuma kara da cewa ya yi jabun satifiket din rajista don yaudarar jama’a su yi rajista da samun shiga makarantar,” in ji Abiodun.
Ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa kimanin dalibai 100 da ba a san ko su wanene ba ne suka shiga kwalejin bayan sun biya Naira 78,000 kowannensu na karatu da sauran kudade.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa, “wanda ake zargin na biyu wanda ya fito daga jihar Enugu kuma yana aiki a matsayin darakta, shi ne ke kula da haramtacciyar makarantar mai malamai kusan 20.”
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin da zarar an kammala bincike.
A wani labarin kuma, ‘Yan Nijeriya Sun Fusata, Jam’iyyun Siyasa Da Dama Za Su Sha Mamaki A 2023 — Obaseki
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da gwamnatoci a kowane mataki, yana mai gargadin cewa masu zabe za su firgita ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa a zaben 2023 mai zuwa.
Da yake zantawa da manema labarai a Benin, babban birnin jihar Edo a ranar Talata, Obaseki ya ce ya kamata ‘yan siyasa su yi tsammanin abin mamaki daga masu zabe saboda rashin shugabanci da kuma rashin iya aiki.