By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a jiya talata tace ta kama wasu mutane 47 da ake zargi da kisan kai daga cikin adadin mutane 1,320 da aka kama bisa laifuka daban-daban a cikin babban birnin jihar tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba 2021.
Yace an kama barayin ne a wurare daban-daban a fadin jihar sannan kuma an kwato makamai da muggan kwayoyi da dama daga wuraren da aka kai farmakin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar jiya a hedikwatar rundunar, dake Ikeja.
Odumosu a lokacin da yake karanta katin shaida na hukumar a cikin watanni biyun da suka gabata ya nanata kudurinsa da jajircewarsa na yin amfani da duk wata hanyar da ta dace don rage laifuka da munanan ayyuka a jihar kamar yadda ‘yan sanda suka bukata.
Sannan yace daga watan Oktoba zuwa Nuwamba 2021, rundunar ta kama mutane 66 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, wanda kuma 72 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da kuma 47 da ake zargi da kisan kai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa rundunar ta kwato makamai 110, alburusai 125 (iri daban-daban) da kuma motocin sata guda takwas.
“Abin sha’awa shi ne, rundunar ta samu nasarar dakile laifuka 46 na fashi da makami a jihar. Rundunar ‘yan sandan a cikin wa’adin daya gabata ta samu damar gurfanar da mutane 151 da ake tuhuma a gaban kotu, daga cikinsu akwai ‘yan daba 15 da ‘yan fashi da makami,” inji shi.
Yace “Tsarin hakan ga fashi a cikin ababen hawa yana kula da shi yadda ya kamata ta hanyar hukumar. Tawagar dabara da sauran rundunonin sirri na rundunar sun hada karfi da karfe domin rage wadannan munanan hare-hare a jihar Legas, tunda babu wata al’umma da ta kubuta daga aikata laifuka.
Hakazalika, saboda yadda ake tantance yawan jami’an tsaro na jihar da kuma tattara bayanan sirri, rundunar ta fara kai farmaki akai-akai, inda bata-gari da ke addabar mutanen jihar Legas da ba su ji ba ba su gani ba suke, musamman hare-hare a kan cunkoson ababen hawa, da yin katsalandan a fadin jihar.” A cewar sa.