Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wasu ‘yan banga guda biyu da ake zargi da yiwa wata mata fyade a kauyen Dogon-ruwa da ke karamar hukumar Ningi a jihar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Rundunar ta kuma ce ta kama wani da ake zargi da yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 3 a kauyen Jimbin da ke karamar hukumar Ganjuwa.
Jaridar Vanguard ta rawaito Kakakin rundunar SP Ahmed Wakil ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talatar nan a Bauchi.
Ya ce, mijin matar ne ya sanar da rundunar ‘yan sandan Ningi kan lamarin.
Karanta kuma: Kotu Ta Tsare Wani Mutum Bisa Yiwa Wata Yarinya Fyade
Wakil ya ce daga baya jami’an tsaro sun kama wadanda ake zargin, Lawali Sule da Babangida Shehu, ‘yan kungiyar ‘yan banga ne wato bijilanti a kauyen Dogon-ruwa.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Agusta da misalin karfe 2 na dare, lokacin da wadanda ake zargin suka hada baki a tsakaninsu tare da kutsawa gidan auren matar dauke da bindigogin gargajiya.
Kakakin ya yi zargin cewa ‘yan bangar sun tambayi mijin nata, wanda baya gida a lokacin, ya yi mata barazana da bindiga kuma yana hada jiki da ita.
Wakil ya ce an dauki wanda abin ya rutsa da ita zuwa babban asibitin Ningi domin duba lafiyarta, inda aka tabbatar da cewa akwai kutsawa.
Ya kara da cewa a yayin bincike, wadanda ake zargin sun amince da aikata laifin da kan su.
Wakil ya ce an kwato bindigogi biyu daga hannun wadanda ake zargin a matsayin hujja.
A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sandan ta kama wani Mato Yohannah mai shekaru 27 da ake zargi da yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 3 a kauyen Jimbin da ke karamar hukumar Ganjuwa.
A cewar Wakil, wanda ake zargin ya amsa cewa wannan ne karo na biyu da ya yi wa karamar yarinya fyade.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce za a gurfanar da mutane ukun da ake zargin domin tabbatar da adalci ga wadanda lamarin ya shafa.
A wani labarin kuma: Jami’an KAROTA Sun Kama Wata Tirela Maƙare Da Giya
Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta cafke wata mota ƙirar Tirela maƙare da Giya, lokacin da ake shirin Kaita masaukinta a Jihar Kano.
Jami’an hukumar KAROTA ne suka sami nasarar cafke motar, lokacin da Direban ke yunƙurin shigowa cikin jihar Kano da misalin karfe 3:00na dare