‘
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami da miyagun kwayoyi da kuma kasancewa mambobin kungiyoyin asiri.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.
Anene ta bayyana cewa kamasu ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da wasu gungun mutane uku da ke kai addabar al’umma a Wurukum, Bankin Arewa da kuma Kasuwar Zamani a Makurdi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Tsare Wani Mutum Da Ya Kashe Kaninsa Da Duka
Ta ce, “Kwamishanan ‘yan sandan jihar Benue, Wale Abass, ya bayar da umarnin bin diddigin wadannan ‘yan fashi da makami a ranar 2/8/2022.
“An yi sa’a, a ranar 26/8/2022 da misalin karfe 1600 na safe, wadanda ake zargin: Fanen Wever, Philip Adanyi, wanda aka fi sani da Baron, da Albert Akor, wanda aka fi sani da J-Boy, dukkansu maza ne, wadanda ba su da wani takamaiman adireshi, an kama su ne a maboyar su dake Logo 1 na yankin Wurukum.”
Ta zayyana kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin, wanda sun hada da bindiga guda daya da aka kera a cikin gida dauke da harsashi guda uku, da kullun ciyawa da ake zargin Tabar Wiwi ve, da sauran miyagun kwayoyi da kuma laya.
Anene ta kuma kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zarginsu da shi.
A WANI LABARI KUMA: Bayan Shafe Kwanaki 174, Ƴan Boko Haram Sun Sako Ma’aikacin Agaji
Mohammed Alkali Imam, ma’aikacin kwamitin ceto na kasa da kasa (IRC) wanda kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da shi a ranar 10 ga Maris, 2022, masu garkuwa da mutane sun sako shi.
An dai yi garkuwa da Imam ne a yankin Monguno da ke jihar Borno a lokacin da wasu mahara suka kai masa hari inda suka kai shi da karfi