Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wasu rikakkun barayi da suka addabi garin Bauchi da kewaye, inda suke shiga gidajen mutane da daddare suna masu fashi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Kamal Datti, Da yake gabatar da ‘yan fashin wa manema labarai ya ce
ana zarginsu da satar mutane domin karbar kudaden fansa da kuma kisan kai.
Kafin nan ma, mutanen sun aiwatar da ayyukan ta’addanci a unguwannin Tudun Salmanu, Water Board Quarters da kuma Unguwar Sarakuna.
Ya ce, wasu daga cikin barayin tuni aka kaisu gaban alkali domin a yanke musu hukunci.