• Rundunar yan sandan jihar Kano ta karyata rahotan dake cewa an Kai wa Sarkin Kano hari.
• A dai yau Lahadi ce ake ta rade-radi cewa an Kai wa Sarkin hari a kafafen sadarwa na zamani.
• Maimagana da yawun rundunar yan Sandar jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shine ya karyata rahoton a cikin wata sanar wa da ya fitar.
Rundunar yan sandan Jihar Kano ta karya ta rahoton da ke ya wo a kafafen sada zumunta na zamani da ke cewa, an kai wa Sarkin Kano Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero hari.
An ta yada rade-radi cewa, an Kai wa Sarkin hari, a kafafen yada sadarwa na zamani da kuma wasu jaridun yanar gizo a yau Lahadi.
Kazalika lokacin da ya ke karyata ya rahotan, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, ” hadarin motane ya afku da motar karshe dake rakiyar Sarkin a yau Lahadi”
DSP Kiyawa ya bayyana cewa, ” Bawai hari aka kai wa Sarkin ba, hadarin motane ya rutsa da motar kashe dake cikin tawagar rakiyar Sarkin na Kano” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masarautar Bichi: An kaddamar da kwamitin da zai kula da auren Dan Shugaban Muhammadu Buhari
“A bisa rashin Sani, lokacin da tawagar Sarkin ke kan hanyar Zaria Road zuwa Fadar shi, sai sugaji wani kara, wanda hakan yasa motocin su ka tsaya cak” a cewar shi.
Bugu da kari, Mai magana da yawun rundunar ya ce” hakan yasa tawagar Sarkin ta bi kasan Gada, Amma sai daya daga cikin motocin ta yi yunkurin zarcewa, bisa tunanin babu wata Mota, inda ba ta sance wa ba, akwai motar karshe na yan rakiyar dake bayanta a cikin tawagar.” Inji Haruna Kiyawa.
Comments 1