Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kashe masu garkuwa da mutane har mutum 8 a daren ranar Alhamis a wani barin wuta da aka gwabza tsakaninsu da jami’an tsaro a karamar hukumar Bali dake jihar Taraba.
Bayan rahotanni da jami’an tsaro suka samu, sak suka zagaye dajin, ko da ganin haka sai suka budewa jami’an tsaro wuta.
Yayin da yake tattaunawa da manema labarai, mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta jihar DSP David Misal, ya bayyana cewa hukumar tasu tayi nasarar samun harsashi da yawa da kuma bindigu kirar AK 47.
“Masu garkuwa da mutanen suna kan hanyar zuwa aikata mumman aikin nasu, a nan ne muka samu rahoto, wanda nan take muka dauki mataki”. Misal ya bayyana.
Ya kara da cewa satin da ya gabata ma hukumar ‘yan sandan jihar tayi nasarar kashe wasu masu garkuwa da mutane su hudu, kuma an kone gawarsu a garin Sabongida dake karamar hukumar Gassol a jihar ta Taraba.