‘Yan sandan jihar Ribas a ranar Litinin sun bayyana cewa sun yi nasarar halaka wani tsagera wanda shi ne shugaban wata gungun wadansu bata gari da suka addabi jihar mai suna Linus Lebari, mai shekara 35, wanda aka fi sani da Bobby ko Devil.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Nnamdi Omoni, shi ne ya bayyana hakana garin Fatakwal, inda ya ce jami’ansu dake ofishin ‘yan sandan Bori sune suka gudanar da wani atisaye inda suka riske su a sansaninsu a wata maboyarsu dake dajin Okwale a iyakar jihar Ribas da Abiya.
‘Yan sandan sun tabbatar da cewa wadannan bata garin ne suka fara harbe-harben kan mai uwa da wabi bayan sun fahimci akwai wadanda suka zo dirar musu. Kakakin ya ce; a nan ne ‘yan sanda suka kare kansu ta hanyar harbe-harbe inda suka yi nasarar raunata wani mai suna Linus Lebari, wanda shi ne shugaban bata garin.
Ya tabbatar da cewa suma a ta janibinsu an raunata jami’an ‘yan sanda biyu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ribas, Mustapha Dandaura, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da kokarin ganin sun dakile ayyukan ‘yan bindiga da bata gari a jihar. Har sai sun tabbatar an yi nasarar kawo karshen ayyukansu a jihar.