Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kashe dan ta’adda guda daya, tare da kwato bindiga kirar AK-47 daya da babura guda hudu da maharan ke amfani da su wajen kai hari a unguwar Mararabar Yakawada da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Katsina SP Gambo Isah, “’yan ta’addan da ba su wuce 30 ba, a kan babura sun tare hanyar Sabuwa zuwa Mararabar Yakawada da nufin yin fashi da garkuwa da mutane.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 200 A Makurdi
“Da samun rahoton, jami’in ’yan sanda na sashen Sabuwa, ya jagoranci rundunarsa zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar, tare da dakile shirin kai harin na maharan.
“A yayin da ake duba wurin, an gano gawar daya daga cikin ‘yan ta’addan da aka kashe, an kuma kwato bindiga kirar AK-47 daya da kuma babura guda hudu daga wurin.” inji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Ambaliyar Ruwa Ta Kori Al’umomi 11 A Jigawa
Akalla al’ummomi goma sha daya suka bar yankunan su sakamakon ambaliyar ruwa a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa.
Shugaban karamar hukumar Shehu Sule Udi ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Ringim.