By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da cewa jami’anta 5 sun mutu a wasu ayyuka daban-daban a fadin jihar, yayin da aka kashe ‘yan bindiga akalla 38 a jihar.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan, Sanusi Buba wanda ya samu wakilcin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Gambo Isah, yace duk da kalubalen da ake fuskanta, rundunar ta samu gagarumar nasara a kan barazanar ‘yan fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran laifuka a jihar.
Ya ce a shekarar 2021 an samu raguwar masu aikata laifuka a jihar idan aka kwatanta da shekarar data gabata.
“A yayin wannan gangamin an kashe ‘yan bindiga talatin da takwas (38) a fadan bindigu daban-daban yayin da jami’an ‘yan sanda biyar (5) suka biya mafi girman farashi.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Rundunar ‘yan sandan ta kama mutane 999 da ake zargi da aikata laifuka 608,Yayin da adadin wadanda aka kama 874 ke fuskantar shari’a a kotunan shari’a daban-daban na jihar,” inji shi.
“An kama mutane 157 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sannan 145 daga cikinsu an gurfanar da su gaban kotu yayin da 12 ake ci gaba da bincike akansu .
“An kama masu garkuwa da mutane sittin da biyar kuma an gurfanar da 63 a gaban kotu yayin da biyu ke kan bincike,” inji shi.
Sannan ya ce an kama mutane 244 da ake zargin barayin shanu ne, daga cikinsu an gurfanar da wadanda ake zargin 230 a gaban kotu yayin da 14 ake ci gaba da bincike akan su.
A cewarsa, an kwato dabbobin gida 1,243 da suka hada da shanu 867, tumaki 352, awaki 24 da kuma jaki daya daga cikin rukunan.
Baya da haka “An kama mutane 246 a cikin shari’o’i 195 da aka ruwaito na fyade da kuma laifukan da suka sabawa dabi’a inda aka ce an ceto mutane 63 a cikin shari’o’in fataucin mutane hudu da aka kai ofishin NAPTIP dake jihar Kano.”
Sannan “An kuma kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su 215 daga hannun ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a lokacin da ake yin nazari.”
“Daga cikin abubuwan da aka kwato a cikin shekarar sun hada da motoci 20 da ake zargin na sata ne; Babura 18 da ake zangin ‘yan fashi sun sace; sai Manyan Bindigu 4; da kuma bindigogin AK 47 44, 1 LAR riffle; Bindiga kirarar G3 guda 1; bindigogi na gida 20; Harsashi 689 da alburusai 7.62mm na AK 47 da harsashi na Anti Air Craft (AA) guda 109.”
Kazalika Kwamishinan ya godewa Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Alkali Usman Baba, “saboda goyon bayan da yake bai wa rundunar, in da ba a kai ga cimma wannan adadi na nasarori ba.”
“Ina kuma kara mika godiyata gareshi bisa yadda aka dauke ni mukami na gaba a matsayin mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (AIG). Babu shakka wanda aka ba da yawa, ana sa ran da yawa. Tabbas zan rama tare da ci gaba da aiki tukuru da sadaukar da kai ga aiki”.
Hakazalika; Kwamishinan ya godewa ’yan jarida bisa gagarumin hadin kai da hadin gwiwa da suke bauwa rundunar.
“Kun nuna gaskiya da nuna ‘yan uwantaka da hadin gwiwa don karfafa zaman lafiya da tsaro a cikin jihar ta hanyar daidaitaccen rahoton ku na ayyukan Rundunar,” in ji shi.
Comments 1