Jami’an yan sanda sun kashe yan bindiga 4 a garin Ilesha dake jihar Osun, a jiya Laraba, kamar yadda rundunar Yan sandan jihar ta bayyana a yau Alhamis.
Tun da fari dai yan bindigan sun farmaki wata Mota ce, dake dauke da wani da ake zargi da kisan Kai, Wanda kuma za’a kai shi cibiyar gyaran hali dake jihar.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Yemisi Opalola a cikin wata sanar wa da ta fitar a garin Osogbo ta babbayana cewa, Yan bindigan sun farmaki motar ne, bayan ta wuce rafin Osunjela akan hanyar ta na Osogbo zuwa Klesa kafin samun nasarar kashe su da rundunar ta yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalejin jihar Kogi ta kori Dalibai 194
Olalola ta bayyana cewa, bakanike na kan gyara motar ce, sai wasu Yan bindiga suka fito daga daji suka bode wa motar wuta, a yunkurin su na kubutar da wanda ake zargi da kisan kai.
Kazalika ta ce, a musayan wutar da jami’an yan sanda suka yi, batagarin sun gudu sun bar babur din su, in da suka afka ciki daji.
A cewar ta, rundunar yan’sandan jihar ta kuma yi nasarar kwato bindiga kirar gida guda 3, da ta zamani 1, sinkin harsasai 14 da dai sauransu.
Kazalika Opalola ta cewa, Yan bindigan uku sun mutu a wani asibiti dake garin Osogbo, sanadiyar Musayan wuta, ya yin da daga bisani a ka cinci gawar guda a cikin daji.
Comments 1