By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, tace jami’anta na Hukumar Leken Asiri ta Tarayya (FIB) da hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta musamman (STS) sun kashe wani dan bindiga da ya yi kaurin suna tare da damke wani mai laifin a Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Muhammad Jalije, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Asabar a Kaduna.
Jalige yace, a ranar 24 ga watan Nuwamba, jami’an rundunar ‘yan sandan Kaduna tare da hadin gwiwar hukumar FIB da STS bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan (CP), Mista Mudassiru Abdullahi, sun yi aiki da sahihan bayanan sirri, inda suka kai samame wata cibiyar da aka fi sani da Sir Joe. Guest House, dake a namba 8 kan layin Sajo dake Unguwan Maigero a cikin Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda aka ce wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari.
A cewarsa, ‘yan bindigar da ake zargin sun yi garkuwa dasu ne, bayan da suka fahimci hatsarin, sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi, sannan suka yi artabu da ‘yan bindigar.
“Wani dan bindiga da aka fi sani da Yellow Magaji, a.k.a Arushe, ya samu rauni a harbin da aka yi masa, yayin da abokin aikinsa Yellow Ashana, da sauran su suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Bayan haka an kai ‘yan bindigar da suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko domin a farfado dasu cikin dan kankanin lokaci domin samun bayanai masu amfani. Amma an tabbatar da mutuwarsa bayan sun isa wajen likita.
Sannan ya bayyana cewa, bayan bincike da aka yi a wurin, jami’an sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK 47 guda daya dauke da alburusai 23 mai girman 7.62 x 39mm, da karin wasu harsashi guda 14 na alburusai da aka ambata da kuma babur Boxer guda daya mallakar barayin.
Jalige yace kwamishinan ‘yan sandan ya jinjinawa kwarin gwiwar jami’an da kuma mahimmin inda aka samu ingantattun bayanai.
Sannan ya bukaci sauran jama’a dasu taimaka wa jami’an tsaro da bayanai cikin gaggawa domin ya ba su tabbacin cikakken sirri yayin aiki da bayanan nasu.