Jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina sun ceto Honarabul Ibrahim Tafashiya dan takarar jam’iyyar PDP a shiyyar Kankia a majalisar dokokin jihar a zaben 2023 mai zuwa.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da dan siyasar a ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Sufeto Gambo Isah ya ce rundunar ta dauki matakin ne tura jami’an ta ne domin kubutar da Dan takarar bayan nan ta samu kiran gaggawar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 4 A Katsina
Ya ce jami’in ‘yan sandan yankin Kankia, SP Ilyasu Ibrahim ne ya jagoranci ‘yan sandan da ke karkashinsa wajen tunkarar ‘yan bindigar inda suka yi artabu da yan bindiga da ya kai ga ceto dan takarar na PDP.
Kazalika, rundunar ‘yan sandan Katsina ta ce ta kuma ceto Salisu Gide, magatakardar Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, wanda aka yi garkuwa da shi tare da matarsa daga gidan su da ke cikin birnin Katsina.
“Abin takaici, tawagar ‘yan sanda ta kasa ceto matarsa daga maharan,” in ji shi.
Sai dai SP Gambo ya ce ana ci gaba da kokarin kubutar da ita da sauran mutanen da ake garkuwa da su, inda ya ce an ga maharan a wani wuri a cikin karamar hukumar Batsari.
A WANI LABARIN KUMA: Machina ya caccaki Kwamishinan Buni kan ayyana Lawan a Matsayin Ɗan takarar Sanata
Kungiyar Yaƙin Neman Bashir Machina ta caccaki Kwamishinan Muhalli na Jihar Yobe, Sidi Yakubu Karasuwa kan ayyana Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar All Progressives Congress APC ta Yobe ta Arewa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Husaini Mohammed Isah ya sanya wa hannu kuma ya mika wa manema labarai.