• Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta kubutar da Fasinjoji 11, da a kayi garkuwa da su a Zamfara.
• An dai yi garkuwa da mutanan ne a jiya Laraba lokacin bikin babbar sallah.
• Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya tabbatar da nasarar kubutar da mutane 11 cikin goma sha 17.
Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta kubutar da Mutum goma sha daya, daga cikin goma sha bakwai, da yan bindiga su ka yi garkuwa dasu a kan hanyar Gusau zuwa Sokoto, ya yin bikin babbar sallah
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta sami sahannun Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Shehu Muhammad.
A cewar sanarwar yan bindigan sun yi garkuwa da mutannan ne a jiya Laraba, lokacin da su ka toshe babban hanyar gwamnatin tarayya, a kusa da garin Dogon Karfe.
Kubutar da mutanan na daya daga cikin nasarar tawagar jami’an yan sanda ta musamman ta samu, bayan an sanar da su faruwan lamarin, inda su ka farwa yan bindiga lokacin da su ke kokarin safaran mutanen da su ka sace, zuwa cikin daji.
Lokacin samamen, sanarwa ta ce, daya daga cikin yan bindigan ya mutu, inda nan take jami’an yan sandan su ka kubutar da Mutum goma sha daya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nigeria da Jihar Kaduna sun yi babban rashin Basarake, inji Sanata Uba Sani
Kazalika sanarwar ta cigaba da cewa, rundunar ba ta sami nasarar tseratar da sauran wadanda yan bindigan su ka yi awan gaba da su ba.
A karshe sanarwar ta ce, an sada dukkannin wadanda aka kubutar da iyalan su.