Rundunar yan sandan jihar Cross Rivers ta kubutar da mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar, cikin awanni 5, bayan sace shi da sanyin safiyar yau Talata, .
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, An yi garkuwa da Oscar Ofuka, mai baiwa gwamna Ben Ayede shawara kan noman cocoa, da misalin ƙarfe 9:30 na safe, a harabar kafar yada labarai ta CRBC, ya yin da ya halarci bode taron Coacoa.
Kwamishinan yan sandan jihar, Sikiru Akande, ya bayyana cewa, rundunar ta dukufa, wurin ganin ta kubutar da Ofuka,
Awanni ƙadan bayan yayi wannan maganar, Akande yace: “Mun samu nasarar kuɓutar da Oscar Ofuka, awanni kadan bayan an yi garkuwa da shi da shi.” Inji Akande.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Yan fim tarbiya suke koya wa” inji Gwammaja
“Yan jarida sun fara zargin mu a kan lamarin, yanzun lokaci yayi da zaku yaba mana,” inji shi.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar kuɓutar da Ofuka ne da misalin ƙarfe 2:30 da rana, a ranar da aka sace shi.
Comments 1