Jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda mai kula yankin Agbarho da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta, sun ceto wani da aka yi garkuwa da su tare da kwato harsashi guda hamsin (50) daga wurin da lamarin ya faru.
Daily Post ta ruwaito cewa, An kubutar da wanda akakaman ne biyo bayan bayanin da jami’in ‘yan sanda na yankin DPO ya samu cewa wasu ‘yan bindiga sun kasance a gidan mamacin da ke kan titin jirgin kasa na titin Agbarho kuma sun yi garkuwa da su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Senegal Ya Nemawa Kasashen Afrika Alfarma A Taron MDD
An samu labarin cewa ‘yan sanda sun yi wa ‘yan fashin kwanton bauna ne.
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta karkashin jagorancin CP Ari Muhammed Ali ta tabbatar da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, DSP Bright Edafe.
Ya ce, “’yan bindigan da suka ga ‘yan sandan sun yi ta harbe-harbe, amma ‘yan sandan sun mayar da martani kuma saboda karfin wuta da ‘yan sandan suka yi, ‘yan bindigar suka gudu suka bar wanda aka sacen.
“An ceto shi ba tare da jin rauni ba. Lokacin da aka binciki wata mota dake wurin, an gano harsashi masu kisa guda hamsin (50).
“Ana ci gaba da kokarin kama ‘yan ta’addan da suka tsere” inji sanarwa.
A WANI LABARI KUMA: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Ariwoola A Matsayin Babban Alkalin Alkalai
Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban alkalin alkalan kasar nan (CJN).
Tabbatar da hakan ya biyo bayan tantance shi da aka yi a zauren majalisar a ranar Larabar nan.