Rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo sun bayyana cewa sun sake kama mutumin nan da ake zargi da kisan kai mai suna Sunday Shodipe, wanda ya tsere daga hannunsu ranar 11 ga Agustan 2020.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Frank Mba, ya ce an sake kama Shodipe ne ranar Lahadi a Bodija da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Idan ba a manta ba, ana zargin mutumin ne da kisan kai daban-daban a yankunan ƙananan hukumomin Akinyele da Moniya da Ibadan.
Sanarwar ta ƙara da cewa Babban Sufeton ‘yan Sanda, Mohammed Adamu ya yaba wa Kwamishinan ‘Yan Sandan Oyo, Joe Nwachukwu Enwonwu da tawagarsa bisa wannan ƙoƙari.