‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Farmakin Da Aka Kai Wa Jami’ar Greenfield, Kaduna
Daga Sulaiman Musa
Shalkwatar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sabon harin da wasu ‘yan bindiga dadi suka kaddamar a kan jami’ar Greenfield da ke Abuja.
Jami’ar wacce take da matsuguni a kan babban hanyar Kaduna-Abuja wanda aka kai harin wajajen karfe 8:35 na daren ranar Talata.
Jami’in watsa labaran ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, shine ya tabbatar da harin wa NAN a yau din nan a Kaduna, yana mai cewa wasu daga cikin daliban jami’ar an yi garkuwa da su.
Jalige ya kuma bayyana cewar har zuwa yanzu ba a ita tantance adadin daliban da aka yi garkuwa da su din ba.
Sai dai tunin ya bayyana cewar an jibge jami’an tsaro a yankin da abun ya faru domin gudanar da bincike da kokarin ceto daliban.