Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da yin garkuwa da Mrs Seriya Raji, mahaifiyar shugaban ma’aikatan gidan gwamnan jihar Yahaya Bello.
A baya Dimokuradiyya ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da Misis Raji a yammacin ranar Litinin a gidanta da ke Nagazi, dake karkashin karamar hukumar Adavi a jihar Kogi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, CP Idrisu Dauda Dabban, ya ce mutanensa sun yi wa yankin da kuma garuruwan kan iyakokin jihar da Edo kawanya da nufin ceto mahaifiyar shugaban ma’aikatan.
Dabban ya ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an kama wadanda suka yi garkuwa da matar, tare da kubutar da wacce aka sace.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci dukkan jami’an ‘yan sanda da su sa kaimi wajen gudanar da bincike da kuma ceto matar.