Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da harin da aka kai a wani shingen binciken ababen hawa na jami’an tsaron hadin gwiwa da ke Amodu a karamar hukumar Nkanu ta Yamma a jihar.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa harin da aka kai da safiyar Talata ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.
KARANTA WANNNA LABARIN: Gobara Ta Hallaka Yara 3 A Fatakwal Tare Da Raunata Wasu
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, PPRO, rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ciki harda Majiyar Jaridar Dimokuradiyya.
Sai dai bai ce uffan ba, kan adadin wadanda suka mutu.
Sanarwar ta ce, “An kai hari a wani shingen binciken jami’an tsaro na hadin gwiwa da ke Amodu a karamar hukumar Nkanu ta Yamma, da safiyar yau 27/09/2022.
“Duk da haka, ina jiran cikakken bayani game da lamarin saboda ci gaba da farautar maharan da suka rufe fuskokinsu, wadanda akasarinsu sun tsere daga wurin da lamarin ya faru da munanan raunukan harbin bindiga, bayanmusayar wuta da tawagar jami’an tsaro.
“Za a sanar da ƙarin bayani nan gaba dakan” inji sanarwar.
A WANI LABARI KUMA: Kotu Ta Yankewa Masu Damfara Ta Yanar Gizo 66 Hukunci A Ibadan
Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta yankewa wasu masu damfara ta yanar gizo akalla sittin da shida (66) hukuncin dauri daban-daban da gidan yari.
Daily Post ta ruwaito cewa, Hukuncin daurin ya kai daga sati biyu, wata hudu da wata shida na yiwa al’umma hidima zuwa wata goma a gidan yari.