Wadansu ‘yan bindiga sun hallaka mutum biyu a yankin Naka, Hedkiwatar karamar hukumar Gwer West a jihar Binuwe.
Kakakin ‘yan sandan jiharm Sewuese Anene ne ya tabbatar da hakana ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar. Anene ya ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da safiyar ranar Lahadi, sai dai ya ce ‘yan sanda sun yi nasarar cafke mutum biyu a wurin da aka kai harin.
“Lamarin dai ya auku da misalin karfe daya na rana”, inji Kakakin.
Har wala yau rahotanni sun nuna cewa na kashe mutum biyar a karamar hukumar Katsina-Ala a jihar a yayin bukukuwan kirsimeti. Wadanda aka kashe din sun hada da ‘yan sanda da kuma farar hula.