Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekaru 21 mai suna Micheal Arigbabuwo, wanda ya rasa ransa a wajen bikin zagayowar ranar haihuwarsa bayan da aka zarge shi da hada wasu kwayoyi masu karfin gaske guda biyu don yin maye
Daily Post ta ruwaito cewa, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Fi Cancanta Ya Zama Zabin Yan Najeriya a 2023, Saraki
Hundeyin wanda ya tabbatar da kame uku daga cikin abokan mamacin ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Ikorodu da ke jihar Legas.
Ya ce bayanan da ‘yan sanda suka samu a Ikorodu sun nuna cewa da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Juma’a ne, aka yi kira da nuna damuwa cewa wasu ‘yan kungiyar masu damfara ta yanar gizo sun kawo gawa zuwa yankin Igbogbo da ke Ikorodu.
“Bisa bayanin, tawagar masu binciken sun ziyarci inda lamarin ya faru kuma suka dauki hoto. An kama wasu matasa uku masu shekaru 23 zuwa 24.
“Wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa marigayin ya sha kwayoyin maye masu karfi gaske kuma ya sha Hodar Ilibis a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar daya daga cikin abokansu da aka gudanar a yankin Igbogbo a Ikorodu.
“Wadanda ake zargin sun kara da cewa marigayin ya fara rikicewa ne nan take a wajam. Inda aka garzaya da shi asibiti amma ya mutu,” inji shi.
Hundeyin ya kara da cewa an dauki gawar an ajiye ta a babban asibitin Ikorodu domin a tantance ta.
Don haka ya gargadi matasa kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, yana mai jaddada cewa, miyagun kwayoyi za su kawo karshen rayuwarsu cikin kankanin lokaci.
A WANI LABARIN KUMA: Zabukan 2023 Zasu Bambanta Da Na 2019 – INEC Ta Fadawa Yan Najeriya
Yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara karatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce za a samu ci gaba wajen gudanar da zaben.
Kwamishiniyar INEC ta kasa mai kula da sa ido da tsare-tsare (PMSC), Farfesa Rhoda Gumus ce ta bayyana hakan, yayin wani taron bita na yini biyu kan Cibiyar Sa ido da Tallafawa Zabe (EMSC) ga shugabannin Sassan Hukumar (HODs) a jiya a jihar Gombe.