Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, sun tabbatar da sace mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda na Suleja wato ACP Musa Rambo.
Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin ‘yan sandan Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya ce an sace ACP din ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Asabar.
Sabo ya ce; a ranar Lahadi jami’an ‘yan sandan atisayen ‘Safe Heaven.’ sun samu motar dan sandar mai lamba KRD 753 BT da katin shaidarsa, da gefen titi.
Ya tabbatar da cewa; ‘yan sandan nab akin mai yiwuwarsu wajen ganin sun ceto ACP din.