Jami’an ‘yan sandan ofishin Kuje, dake birnin tarayya Abuja sun tabbatar da yin garkuwa da mutum hudu wanda wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi a yanki Pegi dake karamar hukumar Kuje.
2-i-c na ofishin ‘yan sandan Insfekta Fidelis Urban, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Nijeriya a ranar Talata a Kuje cewa; an kuma raunata jami’in tsaron NSCDC a lokacin da aka sace mutum hudun.
Fidelis Urban, ya ce jami’in NSCDC din ya samu mummunan rauni da bindiga da kuma adda. Sai dai ya ce tuni aka kwantar da shi a asibitin koyarwa dake Gwagwalada.
Sai dai ya ce tuni rundunar ‘yan sanda suka kaddamar da shirin ‘yanto wadanda aka sace din.